ABNA24 : Al-Dhaif ya ci gaba da cewa; Jagororin gwagwarmaya da dakarun kassam, suna kallon abinda yake faruwa daga kusa, sannan ya ci gaba da cewa; Idan har ba a dakatar da harin da ake kai wa ‘yanuwanmu a unguwar Jarrah ba, to ba za mu nade hannuwanmu mu zama ‘yan kallo ba, masu kai harin za su dandana kudarsu.”
Tun a farkon watan Ramadan ne dai yahudawan sahayoniya su ke kai wa unguwar jarrah hari, da takura musu a lokutan salloli sannan kuma da kokarin tilasta musu yin hijira daga unguwar tasu.
342/